Connect with us

Sports

Pillars Da Heartland Sun Raba Maki A Filin Wasa Na Sani Abacha.

Published

on

Pillars da Heartland sun raba maki a filin wasa na Sani Abacha.

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Kano Pillars ta tashi 2-2 da Heartland a gasar Premier League ta Najeriya da suka kara ranar Lahadi a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata.

Advertisement

Wannan shi ne karon farko da Pillars ta buga wasa a gida tun fara kakar bana, bayan da ta dunga fafatawa a jihar Katsina tun da aka fara kakar nan.

Gwamnatin Tarayya Ta Roƙi Chadi Kada Ta Janye Daga Cikin Ƙasashen Dake Yaƙi Da Boko Haram

Pillars ta zaɓi buga wasanninta a jihar Katsina, sakamakon da aka fara gyaran filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata duk da cewa ba’a ga muciji tsakanin tawagar ta masu gida da kuma katsina united.

Advertisement

Suraju Lawan ne ya fara ci wa Heartland ƙwallo, bayan da suka koma zagaye na biyu daga baya Rabi’u Ali ya warware kallon.

Minti biyu tsakani Heartland ta zura ta biyu a raga ta hannunn Surajo Lawan, wanda yayi nasarar zuwa kwallo biyu a karawar ta hamayya.

Advertisement

Sauran minti 15 a tashi daga fafatawar Pillars tayi nasarar warware kwallon ta hannun babban dan wasanta Ahmed Musa wanda ya bawa kungiyara ta masu gida damar raba maki tsakaninta da kungiyar ta heartland a gaban magoya bayan kungiyar ta kano pillars.

Sakamakon wasannin da aka buga a jiya Lahadi:

Advertisement

 

Ikorodu City City 2-1 Shooting Stars

Advertisement

Enugu Rangers 3-2 Bendel

Sunshine Stars 1-0 Lobi Stars

Advertisement

Abia Warriors 1-1 Enyimba

Remo Stars 0-0 Rivers Utd

Advertisement

Kwara United 2-0 Plateau Utd

El Kanemi 1-0 Niger Tornadoes

Advertisement

Bayelsa United 1-1 Katsina United

 

Advertisement

Ranar Asabar 23 ga watan Nuwamba Pillars za ta ziyarci Lobi Stars a wasan mako na 13 a babbar gasar tamaula ta Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending