News
An Sako Wasu Mata ‘Yan Najeriya Bayan Shafe Watanni 10 Tsare A Saudiyya Bisa Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƙasar Saudiyya ta saki wasu ƴan Najeriya uku, dukkan su mata, da aka kama tare da gurfanar da su gaban kuliya a kasar.
A wata sanarwa da mukaddashin kakakin ma’aikatar harkokin kasashen waje, Kimiebi Ebienfa ya fitar a Abuja a yau Lahadi, sakin ya biyo bayan wata huldar diflomasiya da gwamnatin Najeriya da mahukuntan Saudiyya su ka yi.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Sake Nada Kwamishinoni Biyu Da Ya Sauke
Ƴan Najeriyan uku da suka hada da: Hadiza Abba, Fatima Malah da Fatima Gamboi, an kama su ne bisa zargin mallakar wani abu da ake zargin hodar iblis ce a lokacin da suke aikin Hajji a kasar Saudiyya.
A cewar sanarwar, an kama su ne tare da gurfanar da su a gaban kotu a ranar 5 ga Maris, 2024 a filin jirgin saman Yarima Mohammed bin Abdul Azeez da ke Madinah kuma aka sake su bayan shafe watanni 10 a tsare.
An kama su ne bayan kama wasu mutane biyu sakamakon safarar hodar ibilis, shi ne aka zaci da matan a aikata lefin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, yanzu haka wakilin Nijeriya a Saudiya, Ambasada Muazam Nayaya ne ya karbi matan s Jeddah, inda yanzj haka ake cuku-cukun dawowar su gida Nijeriya.
