Connect with us

News

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Sake Nada  Kwamishinoni Biyu Da Ya Sauke 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin wasu mukamai na wasu muhimman mutane a gwamnatinsa ciki har da Ahmad Muhammad Speaker a matsayin mashawarci kan yada labarai.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce sauran mukaman sun hada da Injiya Ahmad a matsayin mai baiwa gwamna shawara bangaren ayyuka da Malam Sani Abdullahi Tofa bangaren ayyuka na musamman.

Rundunar Sojin Saman Ta Karbi Wasu Jiragen Yaki 12 Domin Ci Gaba Yaki Da Matsalar Tsaro

Gwamnan ya kuma nada Malam Sani Tofa a matsayin Khadi na kotun shari’a, kazalika da da Honarabul Ibrahim Jibrin Fagge a matsayin shugaban hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomi da sai Hajia Ladidi Ibrahim Garko a matsayin shugabar hukumar kula da ma’aikatan jihar Kano.

Sanarwar ta ce, gwamnan zai rantsar da wadanda aka baiwa mukaman a gobe Litinin 6 ga watan Janairun a fadar gwamnatin jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending