Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Yi Kira Ga Yan Jaridu Na Kafar Intanet Da Su Hada Kai Wajen Yada Manufofinta

Published

on

Gwamnatin Kano Za Ta Hada Kai Da Jaridun Yanar Gizo Wajen Yada Manufofinta

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana aniyar ta na hada kai da kafafen yada labarai na yanar gizo domin yada shirye-shirye da manufofinta yadda ya kamata.

Advertisement

Sabon Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a wata ganawa da Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo ta The Association of Online Media Guild ASSOMEG ta hedikwatar ma’aikatar yada labarai ta jihar.

Kungiyar ASSOMEG Ta Taya Ibrahim Waiya Murnar Samun Kwamishinan Yada Labarai Na Jihar Kano

Kwamishinan ya jaddada bukatar yin tsari da hadin gwiwa da kafafen yada labarai na yanar gizo don tabbatar da yada sahihin ayyuka da manufofin gwamnati.

Advertisement

Gwamnati ta aiwatar da ayyuka da yawa, kuma suna bukatar a yada su. ” in ji shi.

Kwamishinan ya kuma yi kira da a hada kai a tsakanin ‘yan jarida na yanar gizo a Kano tare da bayyana shirin horas da dukkanin jami’an yada labarai da jami’an hulda da jama’a na jihar kan tsarin yada Labarai

Advertisement

A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo ta The Association of Online Media Guild ASSOMEG Abdullateef Abubakar Jos, ya bayyana goyon bayansa ga yadda Kwamishinan ya ke bi da kafafen yada labarai. “Mambobinmu kwararru ne, muna nan don taya ku murna, kuma muna goyon bayan matakin da kuka dauka a matsayinku na masu son yada labarai,” inji shi.

Jos ya jaddada bukatar duba lamarin labaran bogi da kuma magance matsala, wadanda ta durkusar da kasashe da dama.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending