Connect with us

News

Nan Ba Da Jimawa Za A Ƙara Kuɗin Kiran Waya Da Data — Gwamnatin Tarayya 

Published

on

Da Yiwuwar Kamfanonin Sadarwa Su Kara Kudin Kiran Waya Da Na 'Data' A Farkon Shekarar 2025

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar cewa za a ƙara kuɗin kiran waya da data, amma ba da kashi 100 kamar yadda kamfanonin sadarwa suka nema ba.

Advertisement

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙi, Dokta Bosun Tijani ne, ya bayyana hakan bayan wata tattaunawa da kamfanonin sadarwa a Abuja.

Bana Yin Shiri Da Shugaba Tinubu Saboda Yana Kawo Manufofin Da Suke Cutar Da Talakawa — Gwamnan Bauchi

Ya ce ana ci gaba da tattaunawa, kuma Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) za ta sanar da sabon tsarin kuɗin nan ba da jimawa ba.

Advertisement

“Mun fahimci buƙatar ƙarin kuɗin, amma ba za a ƙara zuwa kashi 100 ba.

“Burinmu shi ne kare masu amfani da sadarwa tare da tabbatar da cewa kamfanoni suna ci gaba da zuba jari a wannan fanni,” in ji Tijani.

Advertisement

Shugaban NCC na Ƙasa, Dokta Aminu Maida, ya jaddada cewa sabon tsarin zai mayar da hankali kan ɗorewar harkar sadarwa kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito

Ya ƙara da cewa NCC tana aiki don sauƙaƙa tsarin farashi tare da magance ƙorafe-ƙorafen masu amfani da sadarwa.

Advertisement

Kamfanonin sadarwa, ciki har da Airtel, sun bayyana cewa hauhawar farashi ne ya sa ake neman ƙarin kuɗi.

Sun kuma tabbatar wa masu kwastommi cewar za su ci gaba da samun ingantaccen sabis duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending