News
Rikicin Masarutu : Gwamnatin Jihar Kano Ta Ce Ta Gamsu Da Hukuncin Da Kotun Daukaka Kara Ta Yanke
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana matukar gamsuwarta da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke a Ranar Juma’a kan batun masarautar da ta shafi Mai Martaba Muhammadu Sanusi II da Alhaji Aminu Ado Bayero.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Babban Lauyan Gwamnati Kuma Kwamishanan Shari’a, da Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, a ranar Asabar, 11 ga Janairu, 2025, a Cibiyar Yada Labarai ta NUJ.
“A madadin gwamnatin jihar Kano, muna nuna matukar jin dadinmu da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke game da al’amarin masarautar da ya shafi Mai Martaba Muhammadu Sanusi II da sauran bangarorin,” in ji Babban Lauya kuma Kwamishanan Shari’a.
Hukuncin ya soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a baya kuma ya tabbatar da matakin da gwamnati ta dauka game da nadin sarauta da kuma gyara a cibiyoyin gargajiya na jihar Wannan hukuncin ya sake tabbatar da kudurin gwamnati na tabbatar da adalci, yin gaskiya da bin ka’ida a kokarinmu na zamanantar da tsarin gargajiya tare da kiyaye al’adun jihar Kano,” in ji Hon. Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu.
Hukuncin ya kara fayyace hukunce-hukuncen da suka shafi masarautu, tare da jaddada iyakokin tsarin mulki na kotuna a cikin irin wadannan al’amura.
“Hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na soke hukuncin da aka yanke a baya wanda ke nuna shakku kan nade-naden mukaman da jihar ta yi daidai da yadda doka ta tanada, ya kara tabbatar da daidaiton ayyukanmu da kuma karfafa kudurinmu na ci gaba da sauye-sauyen samun wakilci na gaskiya da gudanar da mulki baki daya,” in ji Kwamishinan Yada Labarai.
Domin kaucewa shakku, duk wani hukunci, sanarwa da umarnin da babbar kotun tarayya ta Kano ta yanke, kotun daukaka kara ta yi watsi da ita. “Bugu da ƙari, dokar da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa dangane da masarautu da duk wani mataki da mai girma Gwamnan Jihar Kano ya ɗauka bisa ga wannan doka, kotun ɗaukaka ƙara ta amince da kuma halalta shi.” Inji Hon. Babban Lauya Kuma Kwamishanan Shari’a ya bayyana.
Gwamnatin jihar Kano ta mika godiyarta ga bangaren shari’a bisa yadda suke bin ka’idojin adalci da gaskiya. “Muna mika godiyarmu ga bangaren shari’a kan kiyaye ka’idojin adalci da gaskiya.
Gwamnatin Jihar Kano ta ci gaba da jajircewa wajen yin aiki da cibiyoyin gargajiya, dan tabbatar da zaman lafiya, da samar da ci gaba a dukkan masarautu,” in ji Hon. Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu.
Daga karshe gwamnatin ta bukaci dukkan bangarorin da su mutunta hukuncin kotun, su hada kai da gwamnati domin samar da zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba a jihar Kano. “Muna kira ga dukkan bangarorin da su mutunta hukuncin kotu tare da hada hannu da gwamnati don inganta zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba a jiharmu da muke so. Mu ci gaba da baiwa jihar Kano fifiko fiye da duk wani bukatu na daidaiku,” in ji. Kwamishinan Yada Labarai.
