Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Sanya Hannu A Dokar Da Ta Hana Sojoji Aikata Dukkan Nau’in Baɗala

Published

on

Shugaba Tinubu ya bayyana makomar TETFUND da NITDA da NASENI

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a kan wani kundin dokoki da ya hana sojojin Nijeriya aikata dukkan nau’in baɗala da su ka haɗa da luwaɗi, maɗigo, zinace-zinace, lalata da dabbobi, daudu da sauran dangogin su da ake ganin sun saba wa ka’idojin aikin soja.

Advertisement

Hakazalika dokokin sun hana sojojin ƙasar huda jiki, zanen fata, rashin ɗa’a, da kuma buguwa da barasa a yayin aiki ko bayan aiki.

Rikicin Masarutu : Gwamnatin Jihar Kano Ta Ce Ta Gamsu Da Hukuncin Da  Kotun Daukaka Kara Ta Yanke 

Wannan umarnin na kunshe ne a sashe na 26 na kundin dokokin aikin soja da aka yi wa kwaskwarima, wanda shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a ranar 16 ga Disamba, 2024.

Advertisement

A kwafin takardar kundin da wakilin jaridar PUNCH ya samu a jiya Asabar, wani bangare na kundin na cewa, “An yi ga jami’in soja ya shiga harkar luwadi, madigo, da kuma lalata da dabba.

“Ba zai kasance cikin, ko shiga ayyukan ƴan madigo, luwadi, zina da daudanci ba, gami da shiga ƙungiyar LGBTQ ba.

Advertisement

“Bai kamata jami’in soja ya riƙa huda jiki da kuma yi wa wani bangare na jikinsa zane ba. Jami’i ba zai aikata ko wanne nau’i na rashin ɗa’a, fada, ko wani aiki dai zubar masa da mutunci a idon al’umma ba. Kada jami’i ya bugu a kowane lokaci ko a lokacin aiki ko bayan tashi daga aiki.”

Hakanan kuma dokokin sun haramta wa ko wanne soja shiga harkar kwartanci ko neman matan ma’aikatan da ke ƙarƙashin ofis ɗin su da sauran su.

Advertisement

Sai dai PUNCH ta ce ba a bayyana hukunce-hukunce ko matakan ladabtarwa ga duk wani ma’aikacin da ya karya dokokin ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending