News
Gwamnatin Kano Zata Raba Kayan Makaranta Ga Dalibai Sama Da 700,000 A Fadin Jihar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kammala shirye-shiryen raba kayan sawa kyauta ga daliban da ke makarantun gwamnati a jihar a wani yunkuri na kara magance matsalar yaran da ba su zuwa makaranta.
A cewar kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Kwamared Ibrahim Waiya, dalibai 789,000 maza da mata a makarantun gwamnati 7,092 a fadin kananan hukumomin jihar 44 ne za su karbi kayan makaranta a karkashin shirin.
Shugaba Tinubu Ya Sanya Hannu A Dokar Da Ta Hana Sojoji Aikata Dukkan Nau’in Baɗala
Shirin ya ce an dauki wannan mataki ne da nufin inganta karatun dalibai da kuma tabbatar da cewa duk wani yaro da ya kai shekarun karatu ya samu damar samun ilimi mai inganci, ta yadda za a rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.
Ya kuma kara da cewa shirin zai tallafa wa iyaye marasa galihu da za su fuskanci kalubalen kudi wajen biyan bukatun ‘ya’yansu da kuma kara nuna cewa ilimi ya kasance ginshikin ajandar gwamnatin Abba Kabir Yusuf n
Waiya ya lura cewa, ta hanyar ba da fifiko ga bukatun matasa masu koyo, gwamnati na kokarin karfafawa masu zuwa gaba da kayan aikin da suke bukata don samun nasara tare da bayar da gudummawa mai kyau ga al’umma.
Shirin wanda aka shirya a ranar 13 ga watan Janairun 2025 zai yiwa daliban firamare 1 a fadin jihar kuma ana sa ran zai gudana a dakin taro na Coronation Hall, gidan gwamnati, Kano da karfe 1 na rana.
