Connect with us

Business

Ƴan Pos Na Shirin Ƙara Kuɗi Sakamakon Ƙarin 50% Na Tarho Da Data

Published

on

CBN ya ƙaƙaba wa masu POS ƙa’idoji da dabaibayin yin hada hadar kuɗaɗe, domin bibiyar harƙalla da mazambata
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Masu sana’ar cire kuɗi ta hanyar POS a Nijeriya na iya ƙara farashin ayyukansu sakamakon amincewar gwamnatin tarayya da karin 50% na kuɗin sadarwa.

Mai magana da yawun ƙungiyar ƴan POS na ƙasa (AMMBAN), Ogungbayi Ganiyu ne ya bayyana haka, yana mai cewa ƙarin zai shafi ayyukan masu amfani da wannan tsari, kasancewar suna dogaro da amfani da bayanai da sauran ayyukan sadarwa.

Ɗalibai Northwest Sun Sauya Murnar Kammala Makarantar Su Zuwa Ziyarar Gidan Gyaran Hali A Kano 

Ganiyu ya ce, duk da cewa za su iya ƙoƙarin jure wannan ƙarin, amma yawan kuɗin da ake son cirewa na iya tilasta musu ƙarin farashin don tabbatar da ci gaba da ayyuka. Yayin da ake jiran cikakken tattaunawa akan lamarin, ƙungiyar NATCOMS ta sha alwashin ƙalubalantar karin a kotu.

Advertisement

 

 

 

WIKKI TIMES 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *