News
Gwamnatin Kano Za Ta Ginawa Masu Lalurar Laka Cibiyar Fasahar Sadarwa Domin Inganta Rayuwarsu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada Kudirinta na tallafawa masu bukata ta musamman, musamman masu lalurar laka domin inganta rayuwarsu.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin rabon kayan tallafi da kungiyar masu fama da lalurar laka ta baiwa ya’yan kungiyar da hadin gwiwar gidauniyar MacArthur.
Wani Mahaifi Ya Harbe Yar’sa Sakamakon Yada Bidiyoyinta A Tiktok
Kwamishina Waiya ya ce yana da muhimmanci a tallafawa masu fama da lalurar laka saboda mawuyacin halin da suke ciki sakamakon lalurar da kuma iyalansu.
Ya ba su tabbacin gwamnatin jihar Kano za ta cigaba da fito da tallafin don ingantawa masu lalurar.
Kwamishinan ya ce gwamnatin Kano za ta hada hannu da kungiyar domin samar da cibiyar fasahar sanarwa, sannan a sanya musu kayan aikin a koya musu don inganta rayuwarsu.
A wata sanarwa da daraktan aiyuka na musamman na ma’aikatar yada labarai Sani Abba Yola ya aikowa Kadaura24, ya ce Waiya ya yabawa iyalan wasu lalurar saboda yadda suke tallafawa yan uwansu, sannan ya ba su tabbacin gwamnatin jihar Kano zata cigaba da tallafawa musu don saukaka musu.
-
News7 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News7 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
