News
Hisbah ta kama masoya da su ka ɗaura auren su a gidan cin abinci a Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wani mutum da budurwar sa bisa daura aurensu a gidan cin abinci na Banana da ke titin gidan zoo a Kano.
Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dakta Mujahideen Abubakar, ya tabbatar da kamen ga jaridar PUNCH Online a yau Alhamis, inda ya bayyana cewa jami’an Hisbah sun kai farmaki gidan abincin ne a daren jiya Larabar, biyo bayan samun bayanan sirri.
Godiya Ga Kungiyar Gwamnonin Najeriya Da Suka Yi Gyaran Fuska Ga Kudirin Gyaran Haraji —Dokta Lajada
“Abin takaici ne a gaya muku cewa abokan mutumin ne suka gudanar da daurin auren a gidan abinci ba tare da amincewar iyayen ma’auratan ba,” in ji shi.
Ya yi gargadin cewa hukumar ba za ta nade hannunta ta barin wasu abubuwan da ba a so su ci gaba da keta shari’a a jihar Kano ba
A cewarsa, tun daga lokacin ne hukumar ta kaddamar da farautar dukkan baki da suka halarci haramtaccen daurin auren.
“Mun kama ma’auratan. Muna bin abokan angon da suka gudu daga gidan abincin bayan da jami’an mu suka afkawa wurin,” ya kara da cewa.
Mataimakin kwamandan ya ce ma’auratan sun saba wa dukkanin sharuddan daurin aure, wanda hakan ya saba wa Shari’a.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
