News
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Mayaka Sama Da 5000 Suka Rungumi Shirin Zaman Lafiya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Cibiyar yaki da ta’addanci a ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin tsaro ya ce akalla mayakan boko haram 5000 suka amfana da shirin sake musu tunani da kuma koya musu sana’oi bayan aje makaman su, tare da mayar da su cikin al’umma.
Cibiyar ta kuma tabbatar da cewar babu wasu daga cikin su da suka koma ruwa wajen daukar makamai bayan horo da tallafin da suka samu na watanni 6.
Hisbah ta kama masoya da su ka ɗaura auren su a gidan cin abinci a Kano
Shugabar Cibiyar yaki da tsatsauran ra’ayi Ambasada Mairo Musa Abbas ta bayyana haka a wajen taron gwamnonin jihohin da suka kewaye Tafkin Chadi dake gudana a Maiduguri.
Jami’ar ta ce hada kai da kuma aiki tare zai taimakawa gwamnonin yankin wajen magance matsalolin bai daya da suka addabe su.
Ambasada Abbas ta ce suna hada kai da hukumar wayar da kan jama’a ta kasa a kananan hukumomin Najeriya 774 tare da shugabannin kananan da malaman addini a cikin al’umma wajen sanya ido a kan wadannan tubabun mayaka domin tabbatar basu koma ruwa ba.
Jami’ar ta kuma yabawa matakin da gwamnatin jihar Borno ta bulo da shi na sake tsugunar da mayakan boko haram da suka aje makamansu da ake kira ‘Borno Model’ wanda ya samu goyan bayan majalisar dinkin duniya ganin yadda ya taimakawa shirin gwamnatin tarayya wajen sake sanya wadanda suka tuna a cikin al’umma domin tabbatar da zaman lafiya.
Ambasada Abbas ta ce suna kallon shirin na ‘Borno Model’ a matsayin wanda ya samu gagarumar nasarar karbar wadanda suka aje makamansu da horar da su tare da mayar ad su cikin iyalansu.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
