News
Hasken Waya Da Na Computer Na Kawo Lahani Ga Idanu —kwararren likitan ido
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wani kwararren likitan ido Eugene Maxwell dake garin Warri dake jihar Delta ya yi kira ga mutane da su rika amfani da tabarau domin kare idadunsu daga matsalolin da ake samu a dalilin hasken dake fitowa wayar hannu ko komfuta.
Likitan ya yi wannan kira ne yayin da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Laraba.
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Mayaka Sama Da 5000 Suka Rungumi Shirin Zaman Lafiya
Maxwell ya kuma yi kira ga masu gasa masara, soye-soye da su rika saka hula ko tabarau domin kare idanun su.
Likitan ya yi wannan kira ne ganin yadda yaduwar cututtukan yanar ido ‘Cataracts da Glaucoma’ suka zama ruwan dare.
Ya ce cututtukan na yaduwar ne a dalilin rashin sani da rashin zuwa asibiti domin yin gwajin cutar.
Maxwell ya ce ‘Cataracts’ cutar ce dake kama idon mutum inda mai fama da cutar zai rika ganin kamar yana na rufe masa ido.
Ya ce akan gaji cutar sannan tsufa, busa taba sigari, kwankwadan barasa, kamuwa da cututtuka kamar su ciwon siga na daga cikin matsalolin dake haddasa cutar.
Maxwell ya yi kira ga mutane da su rika zuwa asibiti domin yin gwajin cutar lokaci-lokaci, idan ana fama da da wani cuta kamar hawan jini ko ciwon siga a kiyaye sharuddan cutar sannan a rika amfani da hula da tabarau domin guje wa kamuwa da cututtukan.
Ya kuma shawarci mutane da su rika cin ganyayyaki masu gina jiki, motsa jiki, tare da bin kaidojin likita.
