Connect with us

News

ZAZZABIN LASSA: Mutum 214 sun kamu, 39 sun rasu a cikin makonni uku a Najeriya

Published

on

LASSA FEVER PIX

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Mutum 214 sun kamu sannan wasu mutum 39 sun mutu a jihohi 10 daga ranar 30 ga Disembar 2024 zuwa ranar 19 ga Janairu.

Bisa ga rahoton da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis ya nuna cewa an gano haka ne a kananan hukumomi 43 a kasar nan.

Yan hidimar ƙasa za su fara karɓar sabon alawus na Naira dubu 77 a watan Fabrairu mai kamawa —Shugaban NYSC

Hukumar ta ce a tsakanin wannan lokacin an samu mutum 843 da ake zargin sun kamu da cutar.

Jihohin da cutar ta bullo sun hada Ondo -82, Edo-47, Bauchi -35, Taraba -31, Ebonyi -6, Gombe-4, Kogi-4, Filato-3, Delta-1 da Nasarawa -1.

Mutanen da suka mutu an gano su a jihohin Ondo-8, Edo-9, Bauchi-4, Taraba-9, Ebonyi-3, Gombe-3, Kogi-1, Filato-1 da Nasarawa -1.

Advertisement

Hukumar ta ce an samu ragi a yawan mutanen dake kamuwa da cutar daga mutum 89 zuwa mutum 71.

An gano kashi 77% na mutanen da suka kamu da cutar a jihohin Ondo, Edo da Bauchi.

NCDC ta ce za ta ci gaba da kokari wajen ganin ta dakile yaduwar cutar a kasar nan.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending