News
NDLEA Ta Kai Farmaki Mafakar Ƴan Kwaya A Kano, Ta Kama Mutane 18
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar yaƙi da sha da Fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Kano ta ce ta kama mutane 18 da ake zargi da mallakar muggan kwayoyi daban-daban a jihar.
Mai magana da yawun hukumar, Sadiq Muhammad-Maigatari, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, yana mai cewa an kama su ne a yayin wani sumame da aka kai a wuraren da ake safarar miyagun kwayoyi a Fagge, da Kwarin ƙaya, da ƙofar Wambai da ƙofar Mata.
ZAZZABIN LASSA: Mutum 214 sun kamu, 39 sun rasu a cikin makonni uku a Najeriya
Kwamandan NDLEA na Kano, Abubakar Idris-Ahmad, ya ce an samu adadi mai yawa na wiwi da kuma sinadaran roba masu illa, tare da wasu makamai da aka ƙera a gida.
Ya tabbatar da ƙudirin hukumar na ci gaba da fatattakar ƙungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi da kuma gurfanar da duk masu hannu a irin waɗannan laifuka domin kare al’umma daga hatsarin amfani da muggan kwayoyi.
