Connect with us

News

Yan Sanda Sun Tabbatar Da Sace Muta Ne Goma A Sokoto Suna Tsaka Da Sallar Asuba

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Rundunar ‘yan sandan ta Ƙasa ta ce ta soma farautar ‘yan bindigar da suka sace masallatan goma, a lokacin da suke tsaka da Sallar Asuba a garin Bushe na Sabon Birni dake Jihar Sokoto.

 

Jam’ian tsaron sun ce suna aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa sun ceto mutane da Yan bindigar sukayi garkuwa dasu. Inda suke ikirarin samun nasara a farmakin da suke kai wa maboyar ‘yan bindiga.

Mai magana da yawun ‘yan sandan ta Ƙasa reshen Jihar Sokoto Shi ne ya tabbatar wa da manaiba labarai a ranar Juma’a cewa ‘yan bindiga sun afka garin Bushe ne da sanyin asuba inda suka sace mutanen a lokacin da suke tsaka da Sallar Asubahi.

Advertisement

“Ina so na tabbatar muku da cewa rundunar ‘yan sandan Nijeriya tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro na aiki ba hutawa domin tabbatar da an ceto waɗanda aka sace nan take,” a cewarsa

 

Mazauna garin sun tabbatar da cewa daga cikin waɗanda aka sace har da limamin masallaci a ciki.

 

Haka kuma sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun ɗauki tsawon lokaci suna addabar su duk da cewa akwai jami’an tsaro a garin.

 

Advertisement

A ‘yan kwanakin nan, wasu daga cikin ƙauyuka a Sokoto na fuskantar rashin tsaro musamman ta hanyar hare-haren ‘yan ta’addan Lakurawa da sauran ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.

 

Ko a watan Janairun da ya gabata sai da ‘yan bindiga suka kashe sojoji biyar a Ƙaramar Hukumar Gudu da ke J

ihar Sokoto.

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending