News
Majalisar Dokokin Kano Ta Gayyaci Shugaban Karamar Hukuma Bisa Rushe-Rushe A Kasuwar Rano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gayyaci shugaban karamar hukumar Rano domin bayani kan rushe-rushe da aka gudanar a kasuwar Rano, lamarin da ya haifar da cece-kuce a tsakanin ‘yan kasuwa da al’umma.
Dan-majalisa mai wakiltar karamar hukumar Rano, Alhaji Ibrahim Muhammad Rano, ne ya gabatar da kudiri na gaggawa a zaman majalisar na yau, inda ya bukaci a kai dauki ga ‘yan kasuwar da abun ya shafa.
Rashin Tsaro: Mutum 91,740 Suka Rasa Rayukasu A Najeriya Cikin Shekaru 13 – Rahoto
Alhaji Ibrahim Rano ya bayyana cewa, rushe-rushen da aka gudanar ba tare da wata sanarwa ba ya jefa daruruwan ‘yan kasuwa cikin halin kaka-ni-kayi, wanda hakan ke barazana ga tattalin arzikin yankin.
Majalisar ta amince da kudirin, tare da bukatar shugaban karamar hukumar ya bayyana gaban ta domin karin bayani kan dalilan da suka sa aka gudanar da rushe-rushen ba tare da la’akari da halin da al’umma ke ciki ba.
Wasu daga cikin ‘yan kasuwar da abin ya shafa sun bukaci gwamnatin jihar ta shiga tsakani domin tallafa musu, tare da neman a dakatar da rushe-rushen nan gaba.
Majalisar ta bayyana cewa, za ta ci gaba da bibiyar lamarin don tabbatar da adalci da kare hakkokin al’umma.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
