Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Zargi Shugabannin Ƙananan Hukumomi da Ƙin Buɗe Asusun Banki A CBN

Published

on

Tinubu

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa shugabannin ƙananan hukumomin ƙasar sun ƙi buɗe asusun ajiyar bankuna a Babban Bankin Najeriya (CBN) domin tura musu kuɗaɗen su kai tsaye.

Advertisement

Babbar mai kula da asusun gwamnatin ƙasar, Oluwatoyin Madein, ta bayyana hakan a wani yunkuri na aiwatar da hukuncin kotun koli da aka yanke a ranar 11 ga watan Yunin bara, wanda ke umartar gwamnatin tarayya ta tura kuɗaɗen ƙananan hukumomi ba tare da shiga hannun gwamnonin jihohi ba.

Majalisar Dokokin Kano Ta Gayyaci Shugaban Karamar Hukuma Bisa Rushe-Rushe A Kasuwar Rano

Madein ta ce daga cikin ƙananan hukumomi 774 da ake da su a Najeriya, 25 kacal daga Jihar Delta suka gabatar da lambobin asusun ajiyar bankunansu, yayin da ragowar suka ƙi amsa bukatar.

Advertisement

Rahotanni sun ce gwamnonin jihohi ne ke hana shugabannin ƙananan hukumomi mika lambobin asusun ajiyar domin ci gaba da gudanar da asusun haɗin gwiwa da ke baiwa jihohi damar tafiyar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin.

Gwamnati ta ce tana ci gaba da matsa lamba domin tabbatar da an bi umarnin kotu da ba wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending