Connect with us

News

Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Watan Ramadan A Tarihin Musulunci

Published

on

Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Watan Ramadan A Tarihin Musulunci
Spread the love

DAGA MAIMUNA RABIU UMAR 

Watan Ramadan wata ne mai alfarma da Musulmai ke shafe tsawon watan suna ibadar azumi, ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci.

Baya ga kasancewarsa wata na ibada, Ramadan wata ne da abubuwa masu matuƙar muhimmanci suka faru a tarihin Musulunci, waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen kafa da bunƙasa addinin Musulunci.

Advertisement

Najeriya Ta Matsa Zuwa Matsayi Na Shida A Ƙididdigar Ta’addanci A Duniya Inda A 2024 Aka Kashe Mutane 565

Sheikh Muhammad Mashhud ya yi wa BBC bayani kan wasu muhimman abubuwan da suka faru a watan Ramadan, duk da cewa akwai abubuwa da dama na tarihi da suka faru a watan mai alfarma.

 

1. Saukar da Al-Kur’ani Mai Tsarki

Advertisement

Babban abu mafi muhimmanci da ya faru a watan Ramadan shi ne saukar da Al-Kur’ani mai tsarki. Allah SWT ya fara saukar da Al-Kur’ani a daren Laylatul-Qadr, wanda darajarsa ta fi ta wata dubu. Wannan al’amari ne da ya sanya watan Ramadan ya zama mafi daraja ga al’ummar Musulmi.

 

2. Yaƙin Badar

Advertisement

A ranar 17 ga watan Ramadan, shekara biyu bayan Hijrah, aka fafata Yaƙin Badar, wanda shi ne yaƙin farko a tarihin Musulunci. Duk da cewa Musulmai sun yi ƙasa da makiyan su a yawan sojoji, Allah SWT ya ba su nasara. Sahabbai 14 ne suka yi shahada a wannan yaƙi, kuma aka kashe Abu Jahl, babban maƙiyin Manzon Allah SAW.

 

3. Kwace Makkah (Fathu Makkah)

Advertisement

A ranar 18 ga watan Ramadan shekara takwas bayan Hijrah, Annabi Muhammad SAW ya jagoranci rundunar Musulmai zuwa Makkah, inda suka karɓe ikon garin ba tare da jini ya zuba ba. Wannan nasara ta kawo ƙarshen bautar gumaka a Makkah, kuma mutane da dama suka musulunta bayan hakan.

 

4. Rasuwar Nana Khadija (RA)

Advertisement

Nana Khadija RA, matar farko kuma mafi soyuwa ga Annabi SAW, ta rasu a ranar 10 ga watan Ramadan. Ita ce mace ta farko da ta karɓi Musulunci kuma ta kasance ginshiƙin goyon bayan Manzon Allah SAW a lokacin da yake isar da saƙon Musulunci.

 

5. Rasuwar Nana Aisha (RA)

Advertisement

Nana Aisha RA, ɗaya daga cikin matan Annabi SAW, ta rasu a ranar 17 ga watan Ramadan shekara ta 58 bayan Hijrah. Ta kasance daya daga cikin manyan malamai a Musulunci, inda aka ce ta ruwaito kashi 25% na hadisai da suka shafi addinin Musulunci.

 

6. Rasuwar Sayyidina Ali (RA)

Advertisement

Sayyidina Ali Ibn Abi Talib RA, khalifan Musulunci na hudu, an sari shi da takobi a ranar 19 ga Ramadan kuma ya rasu a ranar 21 ga Ramadan. Ya kasance ɗaya daga cikin fitattun sahabban Annabi SAW kuma gwarzo a yaƙe-yaƙe.

 

7. Yaƙin Tabuk

Advertisement

Yaƙin Tabuk na cikin manyan yaƙe-yaƙe da suka faru a watan Ramadan. Annabi SAW ya jagoranci wannan yaƙi domin yaƙar Rumawa. Yaƙin ya zama wata muhimmiyar alama ta ƙarfafa Musulunci da bunƙasa yawan musulmai.

 

Watan Ramadan ba kawai wata ne na azumi da ibada ba, wata ne da ya cika da abubuwa masu tarihi da suka sauya akalar duniya. Wadannan al’amura sun ƙarfafa Musulunci, kuma har yanzu al’ummar Musulmi na tunawa da su a kowace shekara don ɗaukar darasi da ƙarfafa bangaskiya.

Advertisement

 

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *