Connect with us

News

Najeriya Ta Matsa Zuwa Matsayi Na Shida A Ƙididdigar Ta’addanci A Duniya Inda A 2024 Aka Kashe Mutane 565

Published

on

 

Wani rahoton ƙididdigar ta’addanci na duniya ya bayyana cewa Najeriya ta matsa zuwa matsayi na shida a jerin ƙasashen da suka fi fuskantar ta’addanci a duniya, daga matsayi na takwas da take a shekarun 2023 da 2024.

Rahoton wanda aka fitar ranar 5 ga watan Maris, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, ya nuna cewa mutane 565 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar ta’addanci a Najeriya a shekarar 2024.

Abia, Kano da Ebonyi Sune Kan Gaba Wajen Yawan Yaran da Ba Sa  Kammala Babbar Sakandare – Rahoto

A cewar rahoton, Burkina Faso ce ke kan gaba a matsayin ƙasa mafi fama da ta’addanci, sai Pakistan da Syria a matsayi na biyu da na uku. Kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar ne ke biye, yayin da Najeriya ke matsayi na shida.

 

Sauran ƙasashen da ke cikin jerin ƙasashen 13 da suka fi fama da ta’addanci sun haɗa da Somalia, Kamaru da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.

Advertisement

Rahoton ya nuna cewa yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda da rashin tsaro na ci gaba da ƙara sanya ƙasashen Afirka cikin jerin ƙasashen da ta’addanci ya fi kamaria duniya.

 

 

VANGUARD

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending