Connect with us

News

Shugaban Tinubu Ya  Sauya sunan Jami’ar Kano zuwa Yusuf Maitama Sule

Published

on

images 7

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da sauya sunan Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kano zuwa Yusuf Maitama Sule Jami’ar Ilimi ta Tarayya domin karrama marigayi dan majalisar wakilai kuma jami’in diflomasiyya, Yusuf Maitama Sule.

Advertisement

Sule, an haife shi a Shakarar 1929 kuma ya rasu  a 2017, ya ba da gudummawa sosai ga ci gaban zamantakewa da siyasar Najeriya a tsawon rayuwarsa.

JAMB ta sanar da  Fara Sayar Da Fom Din Shiga Jami’a Kai Tsaye (DE) 

Ya yi aiki a matsayin wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya a New York, inda ya jagoranci kwamitin musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da wariyar launin fata.

Advertisement

Sauran ayyukan da ya yi fice sun hada da zama babban mai shari’a na Majalisar Wakilai ta Tarayya (1954 – 1959), ya jagoranci Tawagar Nijeriya zuwa taron Jihohi masu ‘yanci (1960), ya zama Kwamishinan Korafe-korafen Jama’a na Tarayya na Farko (1976), sannan ya rike mukamin Ministan Ma’adinai da Makamashi.

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar.

Advertisement

Sanarwar ta kara da cewa, “A matsayinta na jami’ar ilimi ta tarayya, za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen horar da malamai, tare da kara karfafa fannin ilimi a Najeriya.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending