News
Sanata Natasha Ta Kai Karar Akpabio Zuwa Majalisar Duniya Ta Kungiyar Majalisun Duniya (IPU)
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar daga Majalisar Dattawan Najeriya, ta daukaka karar dakatarwarta zuwa Kungiyar Majalisun Duniya (IPU) a Majalisar Dinkin Duniya (UN) da ke birnin New York.
Sanatar daga Jihar Kogi, wadda Majalisar Dattawa ta dakatar makon jiya bisa zargin karya dokokinta, ta nemi adalci daga kungiyoyin kasa da kasa da ke kare dimokuradiyya.
Haƙƙin Gyaran Arewa Ba Wai Aikin Shugabanni Ne Kawai Ba Aikin Kowa Ne
A yayin zaman IPU, ta bayyana dakatar da ita a matsayin “ba bisa ka’ida ba,” tana mai cewa an tauye hakkinta na dimokuradiyya.
Bayan jawabinta, Sanata Natasha ta nuna damuwa kan tsaron lafiyarta, tana zargin cewa wasu manyan jiga-jigan siyasa a Najeriya na iya hana ta dawowa daga New York saboda matakin da ta dauka.
-
News21 hours ago
Rundunar ‘Yansanda Ta Yi Gargaɗi Gam Da Yiwuwar Kai Hare-hare Makarantu Da Wuraren Ibada
-
News5 days ago
Dakarun Soji Cafke Wani Shugaban ’Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Harsasai 300
-
News6 days ago
Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu
