News
Ango Da ’Yar Uwar Amarya Sun Rasu Mintuna 30 Kafin Daurin Aure A Bauchi
A wani mummunan hatsari da ya jefa iyalai da al’umma cikin alhini, wani ango, Abba Musa, da ’yar uwar amaryarsa, Raihanatu Sulaiman, sun rasa ransu mintuna 30 kafin a daura aurensa a garin Boto, karamar hukumar Tafawa Balewa, Jihar Bauchi.
Hatsarin ya faru ne yayin da angon tare da amaryarsa, Maryam Sulaiman, da wasu mutum uku ke tafiya zuwa ƙauyen Murno domin gaisawa da ’yan uwan amarya, kamar yadda al’adar Hausawa ta tanada.
Wani mahaukaci da ya yi yunkurin tsallaka titi ya haddasa hatsarin, inda direban ya kasa shawo kan motar, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar angon nan take, sannan Raihanatu ta rasu a asibiti.
Duk da cewa amaryar da sauran fasinjoji sun tsira da raunuka, mutuwar angon da ’yar uwarta ta jefa dangin biyu cikin jimami. Mahalarta daurin auren da suka hallara don bikin sun rikice, inda gidan da aka tanada don walima ya koma wurin makoki.
Rahotanni sun nuna cewa mahaifin angon ya yanke jiki ya fadi daga tashin hankali, inda aka garzaya da shi asibiti sakamakon hauhawar jininsa kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito.
Haka nan, mahaifiyar angon ta suma lokacin da aka ba ta labarin rasuwar ɗanta.
A ƙarshe, bayanai sun tabbatar da cewa an yi jana’izar mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, yayin da amaryar ke cikin mawuyacin hali—jiki na fama da rauni, zuciya kuma cike da radadin rashin masoyi da ’yar uwa a ranar da ta kamata ta kasance mafi farin ciki a rayuwarta.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
