Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Gwamnan Rikon Kwarya A Jihar Rivers

Published

on

1742324759623

 

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Vice Admiral Ibokette Ibas (mai ritaya) a matsayin sabon gwamnan rikon kwarya na Jihar Rivers na tsawon watanni shida.

Advertisement

Idan za a iya tunawa, Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa, tare da majalisar dokokin jihar, bayan da aka ayyana dokar ta-ɓaci a jihar saboda rikicin siyasa da ya daɗe yana addabar yankin.

 

Advertisement

A cikin jawabin da ya gabatar, shugaban kasa ya bayyana cewa, bayan nazari da duba halin da ake ciki, dole ne a aiwatar da sashi na 305 na kundin tsarin mulki domin tabbatar da doka da oda a jihar Rivers daga yau, 18 ga Maris, 2025.

Shugaba Tinubu ya dakatar da gwamnan Rivers da mataimakin sa da yan majalisar jihar na watanni 6.

Tinubu ya ce ya yi iyakar kokarinsa don warware matsalar siyasar da ke tsakanin gwamnan da majalisar dokokin jihar, amma dukkan ɓangarorin sun yi watsi da yunkurin sasanci. Haka nan, shugaba ya bayyana cewa, wasu jiga-jigan siyasa sun yi ƙoƙari wajen samar da mafita, amma har yanzu babu wata sahihiyar gwamnati a jihar.

Advertisement

A saboda haka, gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin dakatar da gwamnan da mataimakiyarsa na tsawon wata shida, tare da naɗa Vice Admiral Ibokette Ibas domin jagorantar jihar har zuwa lokacin da za a kammala tantancewar da kuma samar da cikakken shiri na siyasa

a jihar.

Advertisement

 

 

Advertisement

SAHARA REPORTS 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending