News
Zargin Cin Hanci: ‘Yan Majalisa Sun Karbi Dala 25,000 Kowane Don Goyon Bayan Dokar Ta-Baci
Ana zargin an baiwa yan Majalisun Najeriya cin hanci domin su goyi bayan dokar ta bacin da shugaban ya sanya a jihar Rivers
Wata majiya da ga Jaridar PEOPLE GAZETTE ta ruwaito an baiwa wasu daga cikin yan majalisun makudan kudade domin kada su baiwa Shugaban kasar kunya idan an zo kada kuri’a a yau Alhamis
Manyan ‘Yan Adawar Najeriya Sun Bukaci Majalisa Ta Yi Watsi da Bukatar Shugaba Tinubu Kan Rivers
Wasu daga cikin yan majalisar bayan sun amshi na goro sun ki zuwa majalisar a zaman da za a yi a kan dokar a yau Alhamis
Advertisements
