News
Yan Daba Sun Kashe Matashi Mai Shekaru 23 A Masallaci A Kaduna
Wani matashi mai shekaru 23, Usman Mohammad, ya rasa ransa bayan da wasu ‘yan daba suka kai wa masu hari yayin sallar Tahajjud a Layin Bilya, titin Makwa, Rigasa, Jihar Kaduna, a daren Juma’a.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa jami’an tsaro sun samu kiran gaggawa da misalin karfe 2:00 na dare a ranar 21 ga Maris, 2025, kan harin da wasu miyagu suka kai daga wurare daban-daban.
A cewarsa, kafin jami’an tsaro su isa wurin, ‘yan daban sun riga sun daba wa Mohammad wuka mai tsini.
An garzaya da shi asibiti domin ceto ransa, amma daga bisani ya rasu sakamakon munanan raunukan da ya samu.
Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun cafke mutane 12 da ake zargin suna da hannu a harin, inda suka amsa laifinsu.
Haka kuma, an kwace makamai daga hannunsu, yayin da ake ci gaba da bincike domin gurfanar da duk masu hannu cikin lamarin a gaban shari’a.
Bisa wannan mummunan hari, rundunar ‘yan sandan Kaduna ta kara tsaurara matakan tsaro a wurare masu muhimmanci, musamman masallatai, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
