Connect with us

News

Kotu Ta Tura Matashi Gidan Gyaran Hali Bisa Zargin Jagorantar ‘Yan Daba A Kano

Published

on

Kotu

Wata kotun majistare da ke Kano ta tura wani matashi mai suna Salmanu Yakubu gidan gyaran hali, bayan da aka gurfanar da shi bisa zargin mallakar wuka da kuma jagorantar ‘yan daba.

An gurfanar da Salmanu ne a gaban kotun majistare mai lamba 11 da ke zamanta a  Airport, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Zubairu Inuwa.

Advertisement

Yawan Yara Marasa Zuwa Makaranta Ya Ƙaru A Kano — Bincike

A cewar ‘yan sanda, ana kuma zargin matashin da yunkurin raunata wani jami’in ‘yansanda yayin wani rikici, sai dai ya musanta tuhumar da ake masa.

Kotun ta buƙaci a kawo jami’in bincike domin cigaba da sauraron shari’ar, inda aka ɗage zaman shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Yuli.

Advertisement

A wani zaman daban da kotun ta yi, ta bayar da belin wasu matasa da ake zargi da haɗa baki wajen tayar da tarzoma da amfani da makamai wajen karɓe wayoyin jama’a.

An ce an kama matasan ne a unguwar Dorayi, yayin wani rikici da ake zargin su da hannu a ciki, sai dai suma sun musanta zarge-zargen da ake musu.

Advertisement

Mai shari’a Zubairu Inuwa ya bayyana cewa kotun ta amince da belin matasan, amma bisa wasu sharudda.

Daga cikin sharuddan da kotun ta gindaya har da buƙatar kowanne daga cikin matasan ya gabatar da mahaifinsa da kuma babban sakatare a kowace ma’aikata da ke Kano a matsayin masu tsaya masa. Dole ne su kawo hotuna biyu na masu tsayawa musu.

Advertisement

Kotun ta ce idan wani daga cikinsu ya tsere, masu tsaya musu za su biya tarar Naira miliyan ɗaya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending