News
Bututun Iskar Gas Ya Sake Fashewa A Ribas: Wata Gobara Mai Ƙarfi Ta Tashi
Wata fashewar bututun iskar gas ta sake aukuwa a jihar Ribas, abin da ke ƙara dagula lamarin tsaron makamashi a yankin. Wannan fashewa ta faru ne a wurin ajiyar man fetur na Soku, da ke ƙaramar hukumar Akuku Toru, kamar yadda ƙungiyar kare muhalli ta YEAC-Nigeria ta tabbatar.
A cewar sanarwar da Daraktan ƙungiyar, Dr. Fyneface Dumnamene Fyneface, ya fitar, wasu matasa ne suka fara bayar da rahoton fashewar da ta auku da safiyar Lahadi. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an ga walkiya mai ƙarfi da harshen wuta a sararin sama, kuma har zuwa lokacin rahoton, gobarar na ci gaba da ci.
An Kama Soja Da Ɗan Sanda Bisa Zargin Satar Batiran Jirgin Ƙasa A Kaduna
Rahotanni sun nuna cewa wurin da fashewar ta faru yana ƙarƙashin kamfanin iskar gas na ƙasa (NLNG), kuma yana da wahalar shiga. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da musabbabin fashewar ba, duk da cewa ana zargin matsalar kayan aiki, harin da aka kitsa ko kuma ɓarnar ‘yan ta’adda.
Wannan shi ne karo na uku da ake fuskantar irin wannan fashewa a cibiyoyin man fetur a jihar Ribas cikin mako guda.
A baya, fashewa ta auku a Ogoni da kuma Oga/Egbema/Ndoni LGA. Hakan ya sanya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ayyana dokar ta-ɓaci tare da dakatar da Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, da wasu jiga-jigan gwamnatin sa.
Ƙungiyar YEAC ta buƙaci hukumar NOSDRA da ta gudanar da bincike na gaggawa domin gano ainihin dalilin fashewar, tare da tabbatar da hukunta duk masu hannu a lamarin bisa tanadin dokar harkokin man fetur ta 2021 (PIA).
