Connect with us

News

Jami’an Hukumar NDLEA Sun Cafke ‘Yar Indiya Da Hodar Iblis Kilogiram 11 A Filin Jirgin Kano

Published

on

Jami'an Hukumar NDLEA Sun Cafke ‘Yar Indiya Da Hodar Iblis Kilogiram 11 A Filin Jirgin Kano

Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, NDLEA, sun cafke wata mata ‘yar kasar Indiya mai suna Neetu Neetu, ‘yar shekara 42, a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano dauke da hodar iblis mai nauyin kilogram 11 da aka boye a cikin ledodi masu kamannin kwallan cokolate.

An kama Neetu ne yayin da jami’an NDLEA ke bincike kan sahihan bayanan sirri da suka samu yayin shigowarta daga jirgin Qatar Airways QR1431 daga Bangkok, Thailand ta Vietnam da Doha, a ranar Juma’a 14 ga Maris 2025.

Advertisement

Mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina Ta Rasu Tana Da Shekaru 93

Hukumar ta bayyana cewa an samu bayanan sirri kafin kama ta, wanda hakan ya sa aka yi mata bincike mai zurfi har aka gano muggan kwayoyin da aka ɓoye.

Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Rtd), ya bayyana cewa wannan kama wata alama ce da ke nuna yadda ‘yan kasuwar miyagun kwayoyi ke ƙara amfani da bakin-haure wajen shigowa da kayan maye cikin Najeriya. Ya kuma yaba da kokarin jami’ansa na dakile irin waɗannan haramtattun ayyuka.

Advertisement

 

 

Advertisement

STALLION TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending