News
Ma’aikatan Muryar Amurka (VOA) Sun Maka Trump a Kotu
Wasu ma’aikatan gidan rediyon Muryar Amurka (VOA) sun kai ƙara a kotun tarayya da ke Manhattan, inda suka zargi tsohon Shugaban Amurka Donald Trump da babbar mai ba shi shawara, Kari Lake, da take haƙƙinsu.
Sun ce matakin rufe gidan rediyon ba zato ba tsammani ya saɓa wa dokar ƙasa. Masu shigar da ƙarar, ciki har da tsohon shugaban ofishin White House na VOA, Patsy Widakuswara, da Editar Press Freedom, Jessica Jerreat, suna neman a mayar da ma’aikatan fiye da 900 da kuma na wucin-gadi 550 bakin aikinsu.
Nan da Wata Shida Za a Kammala Ginin Majalisar Dokokin Jihar Rivers – Ibas
Sai dai Lake ta kare matakin, tana mai cewa ma’aikatar tana fama da ɓarna da cin hanci, don haka bai dace kuɗin haraji na Amurkawa su ci gaba da daukar nauyinta ba.
Tun bayan rufe VOA, shafin intanet da rediyon sun kasance a yi shiru ba tare da sabbin labarai ba.
