Connect with us

News

Masu Haƙar Kaburbura Sun Koka Kan Ƙarancin Alawus Da Matsalolin Maƙabarta A Kano 

Published

on

13554dfb 998d 4d9b 9396 14880ac78274.jpg

Masu haƙa kaburbura da gyara maƙabarta a Kano sun koka kan ƙarancin alawus ɗin da ake ba su, wanda ya ragu daga N5,000 zuwa N3,000 ko ma ƙasa da haka a wasu lokuta.

Malam Suleiman Mohammed, wani mai haƙar kabari a maƙabartar Tudun Wada, ya bayyana cewa a wasu lokutan ana shafe watanni ba tare da an biya su ba. Ya ce sun kai ƙorafinsu gaban Sarkin Kano, inda aka yi musu alƙawarin duba lamarin.

Advertisement

Masu Tauna Cingam Na Haɗiye Ƙananan Robobi Ba Tare Da Sun Sani Ba – Masana

A cewarsa, aikin haƙa kabari yana da hatsari kuma yana da buƙatar ƙarfi, don haka yana da kyau a inganta alawus ɗinsu. Bugu da ƙari, ya koka kan yadda ɓata gari ke amfani da maƙabarta wajen shaye-shaye da adana makamai kamar yanda ya shidawa BBC

Ya nemi a inganta ayyukansu ta hanyar tsaftace maƙabartar da gyara katangarta da sanya fitulu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending