Connect with us

News

Yan Sandan Kano Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Kai Wa Sarkin Kano Hari, Da Kisan Ɗan Bijilanti

Published

on

Yan sandan Kano sun Kama Wanda Ake Zargi Da Kai Wa Sarkin Kano Hari Da Kisan Ɗan Bijilanti

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Usman Sagiru, mai shekaru 20, daga unguwar Sharifai, bisa zargin kashe wani jami’in Vigilante da kuma raunata wani a lokacin da suke ba wa Mai Martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi II, kariya bayan Sallar Idi a ranar Lahadi, 30 ga watan Maris, 2025.

Bisa bayanan ’yan sanda, an ce Usman Sagiru tare da wasu da har yanzu ba a kama ba, sun daba wa Surajo Rabiu daga unguwar Sabon Titi Jaba Quarters wuka, wanda daga bisani ya rasu sakamakon raunukan da ya samu. Haka kuma, wani jami’in Vigilante, Aminu Suleman daga Kofar Mata Quarters, ya ji raunuka kuma yana karbar magani a Asibitin Murtala Mohammed da ke Kano.

Advertisement

MURNAR SALLAH: Mu Ci Gaba Da Rayuwa Cikin Zaman Lafiya Da Soyayya – Amb. Bello Sani Maitakalma

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta fara bincike kan lamarin, tare da kiran Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, don yi masa tambayoyi.

Haka kuma, rundunar ta jaddada haramcin gudanar da kowanne irin Hawan Sallah, tare da gargadin cewa duk wanda aka kama yana aikata hakan ko kuma yana aikata ta’addanci da ka iya haddasa tashin hankali, zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Advertisement

A karshe, ’yan sanda sun bukaci al’ummar Kano da su kwantar da hankalinsu tare da bada hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending