News
Shehu Sani Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Gilla A Edo, Ya Bukaci Hukumomi Su Dauki Mataki
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani, yayi Allah wadai da kisan yan Arewa a jihar Edo, ya bukaci ayi musu Adalci tare da samar da zaman lafiya
Da yake jawabi a gidansa da ke Kaduna yayin bikin Sallar Edil-Fitr a ranar Lahadi, Sanata Sani ya yi tir da kisan gilla da aka yi wa wasu mafarauta a jihar Edo. Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta kamo masu laifin tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
SANKARAU: Mutum 60 Sun Rasa Rayukansu A Kebbi, Barazanar Yaduwar Cutar Na Karuwa
“Idan ‘yan kasa ba za su iya yin yawo cikin ‘yanci a ƙasarsu ba, to wannan na nufin ba mu zama ƙasa ta gaske ba. Idan kuma mutane na daukar doka a hannunsu bisa kowace dalili, to hakan yana nuna babu gwamnati ko wani iko,” in ji shi.
Sani ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da ke kishin ƙasa da su hada kai don tabbatar da zaman lafiya da hadin kai, domin kare dimokuradiyya duk da matsalolin da ake fuskanta. Ya nanata cewa gwamnati dole ta mutunta ‘yancin dan Adam, musamman ‘yancin rayuwa, wanda ke da matukar muhimmanci wajen tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaban kasa.
