Connect with us

News

Kwacen Waya Da Fadan Daba Ya Haifar Da Zaman Dardar A Unguwanni Da Dama A Cikin Kano

Published

on

Fadan Daba Ya Haifar Da Zaman Dardar A Unguwanne Da Dama A Cikin Kano

Al’ummar unguwar Gobirawa Dukawa Titin ‘Yan Smogal a ƙaramar hukumar Dala dake Jihar Kano  na cigaba da zaman ɗar-ɗar sakamakon yadda wasu samari ɓatagari ke neman mayar da yankin wata ƙaramar Sambisa. Wannan matsala ta samo asali ne daga faɗace-faɗacen daba da kuma kwace waya da ake yawan samu a yankin a ‘yan makwannin nan.

Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa Lamarin na ci gaba da haifar da matsala ga masu gudanar da kasuwanci da sauran mazauna yankin. Wani matashi  bayyana cewa matsalar na hana mutane walwala da gudanar da harkokinsu yadda ya kamata.

Advertisement

Kisan Edo: Jami’an Hukumar DSS Sun Kama Manyan Mutane Biyu Da Ake Zargi

Malam Hassan Madaki, shugaban shiyya ta uku na masu aikin sintiri na ƙaramar hukumar Dala, ya bayyana irin matakan da suke ɗauka don tabbatar da zaman lafiya. Ya ce suna aikin sintiri akai-akai domin rage yawaitar irin waɗannan ayyuka.

A nasa ɓangaren, Dagacin Gobirawa, Musa Isah Muhd, ya bayyana cewa suna ƙoƙarin sulhunta waɗanda ke shiga faɗace-faɗace. Sai dai ya yi gargaɗin cewa duk wanda yaƙi karɓar sulhu, ba shakka za a ɗauki matakin ladabtarwa a kansa.

Advertisement

Honarabul Suraj Ibrahim Imam, shugaban ƙaramar hukumar Dala, ya nuna takaicinsa kan wannan matsala. Ya ce suna aiki tukuru don magance matsalar, tare da shawarci al’ummar yankin da su kasance masu kare kansu kafin isowar jami’an tsaro.

Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin ‘yan sanda, amma mai magana da yawun su, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa yana halartar wani taro, kuma zai tuntube mu bayan ya kammala.

Advertisement

Al’ummar yankin na fatan cewa za a ɗauki matakin gaggawa don dakile matsalar, domin su samu damar ci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending