Connect with us

News

‘Yan Sanda Sun Gayyaci Sarki Sunusi Kan Rikicin Da Aka Samu A Tawagarsa A Ranar Sallah

Published

on

images (1)

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gayyaci Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, domin amsa tambayoyi kan rikicin da ya auku yayin hawan Sallah da ya gudana karkashin kulawarsa, wanda ya haifar da mutuwar wani matashi.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan sashin bayanan sirri, Olajide Rufus Ibitoye, ya sanya wa hannu, rundunar ta bayyana cewa gayyatar na da nufin gudanar da cikakken bincike kan yadda lamarin ya faru da kuma gano hakikanin musabbabin rikicin.

Advertisement

Bashin Najeriya Ya Kai Naira Tiriliyan N144.67 A 2024 – Rahoton DMO

Sanarwar ta bukaci Sarkin da ya bayyana a shelkwatar ‘yan sanda da ke Abuja a ranar Talata, 8 ga Afrilu, 2025 da misalin karfe 10:00 na safe. An bayyana cewa umarnin gayyatar ya fito ne daga Babban Sufeton ‘yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun, domin tabbatar da gaskiya da adalci game da lamarin da ya girgiza al’ummar Kano.

Rundunar ‘yan sanda ta ce wannan mataki na daga cikin kokarinta na tabbatar da doka da oda, tare da tabbatar da cewa kowane dan kasa yana da alhakin bayyana bayani idan bukatar hakan ta taso, ba tare da la’akari da matsayinsa a al’umma ba.

Advertisement

Lamarin rikicin da ya auku cikin tagawar sarkin yayin hawan Sallah ya janyo cece-kuce a fadin kasar, inda aka ruwaito mutuwar wani matashi. Wannan ya kara jaddada bukatar gudanar da bincike mai zurfi domin gano gaskiyar lamarin.

Rundunar ta bukaci jama’a da su kwantar da hankula tare da bai wa hukumomi hadin kai wajen tabbatar da gaskiya da adalci.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

PREMIER RADIO 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending