Connect with us

News

‎Madalla Da Ganduje Gwarzon Zaman Lafiya, Mai Kishin Ƙasa Da Kishin Kano. ‎ ‎

Published

on

FB IMG 1743947239117

DAGA ABBA ANWAR

‎Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sake bayyana kansa a matsayin gwarzon zaman lafiya a yayin wata ziyarar Sallah da kuma gaisuwar rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, ga Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Advertisement

‎A cikin jawabinsa, Ganduje ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai, inda ya yaba wa Sarkin Kano bisa hikimar gujewa rikici ta hanyar soke Hawan Sallah, matakin da aka ɗauka bisa shawarwarin malamai da dattawan Kano.

Shugaba Tinubu Ya Bayar Umarnin A Kamo Maharan Da Suka Kashe Mutane Fiye Da 50 A Filato.

‎ “Mun zo gaisuwa da taya Sallah, amma muna yabawa da yadda ka kaucewa zubar da jini wajen ɗaukar matakin da ya dace,” in ji Ganduje.

Advertisement

‎Tsohon gwamnan na Kano ya tuna da irin rawar da ya taka a wanzar da zaman lafiya a lokacin gwamnatinsa, musamman yadda ya haɗa matasan Arewa da shugabannin kabilar Igbo domin hana rikicin ƙasa, lamarin da ya sa aka ba shi lambar girmamawa daga Kudu maso Gabas – Aguna Echemba I.

Advertisement

‎Ya kuma bayyana yadda gwamnatinsa ta mayar da dajin Falgore daga mafakar masu laifi zuwa filin horas da sojoji, tare da kafa cibiyoyin tsaro irinsu dakin lura da na’urori, cibiyar tsaro a Rijiyar Zaki da kuma ɗakunan kwana a kowane ƙofar shiga Kano don dakile masu shigowa da laifi.

Advertisement

‎“Ganduje mutum ne mai ɗauke da sakon zaman lafiya a ko’ina,” in ji marubucin, “tun daga lokacin da yake mataimakin gwamna har zuwa zamansa gwamna, da kuma yanzu a matsayin shugaban jam’iyyar ƙasa. Yana zaune lafiya da kowa kuma yana ƙoƙarin kawo zaman lafiya a jam’iyya da ƙasa baki ɗaya.”

Advertisement

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending