Connect with us

News

Amnesty International Ta Yi Allah-wadai Da Tarwatsa Masu Zanga-zanga A Najeriya

Published

on

d25da7e0 1414 11f0 a75e ed2c16a46018.jpg

Kungiyar kare haƙƙin ɗan’adama ta duniya, Amnesty International, ta bayyana damuwa matuƙa da kuma yin Allah-wadai da yadda jami’an tsaron Najeriya suka tarwatsa masu zanga-zanga cikin ƙarfi da karfi a wasu manyan biranen ƙasar.

A ranar Litinin ne daruruwan ƴan Najeriya suka fito zanga-zanga cikin lumana domin neman shugabanci nagari, a ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Take It Back. Zanga-zangar ta bazu zuwa birane kamar Abuja, Legas da Fatakwal, duk da gargaɗin da rundunar ‘yan sanda ta bayar kan gudanar da irinta.

KATSINA: Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 4, Sun Sace 45 

Sai dai a wasu daga cikin waɗannan wurare, jami’an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar ta hanyar harba hayaƙin mai sa hawaye. An kuma samu rahotannin kama wasu daga cikin masu zanga-zangar, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta da kuma daga masu rajin kare haƙƙin ɗan’adama.

Daraktan Amnesty a Najeriya, Malam Isah Sanusi, ya bayyana cewa kungiyar na gudanar da bincike don tantance adadin waɗanda aka kama da kuma yadda aka mu’amalantar da su. A cewarsa:

> “Wannan abin kunya ne kuma abin takaici. Mutane sun fito cikin lumana amma aka nuna musu ƙarfi. Mun yi Allah-wadai da wannan matakin.”

“Ba za a samu zaman lafiya ba har sai mutane na da ‘yanci su bayyana ra’ayinsu, musamman kan yadda ake tafiyar da ƙasar. ‘Yan Najeriya na da haƙƙin zanga-zanga cikin lumana kamar yadda tsarin dimokuraɗiyya ya tanada.”

Advertisement

Kungiyar Amnesty ta kuma yi kira ga gwamnati da ta daina take haƙƙin jama’a wajen gudanar da zanga-zanga, musamman idan ana yin hakan cikin lumana da bin doka.

A gefe guda, rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta bayyana cewa zanga-zangar ta zo ne a daidai lokacin da aka ware a matsayin ranar bikin ‘yan sanda, wato 7 ga watan Afrilu. Wannan, a cewar sanarwar rundunar, ya sa suka nuna damuwa da shirin gudanar da zanga-zangar a wannan rana.

Tarzoma tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga ba sabon abu ba ne a Najeriya, musamman idan zanga-zangar na ɗauke da saƙon adawa da manufofin gwamnati. Wannan lamari ya sake ɗaga hankali da kira daga sassa daban-daban na duniya kan buƙatar kare ‘yancin faɗar albarkacin baki da gudanar da zanga-zanga ba tare da tsangwama ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending