Connect with us

News

Mata Biyu Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Faɗawa Kudiddifi A Kano

Published

on

images

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu mata biyu sakamakon faɗawa cikin wani ramin kudiddifi da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar.

Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aike wa jaridar Inda Ranka a daren Talata. Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata, yayin da aka samu kiran gaggawa daga shugaban jami’an sintiri na karamar hukumar Gezawa.

SATAR KAYAN MAKARANTU: Hukumar NSCDC Ta Kama Mutane Biyar A Kano

A cewarsa: “Da misalin ƙarfe 11:15 na safiyar jiya ne muka samu kiran neman agaji, inda aka bayyana mana cewa wasu mata biyu sun faɗa cikin kudiddifi tun daren Litinin. Nan take muka tura jami’anmu domin gudanar da aikin ceto.”

Bayan isar jami’an hukumar, an samu nasarar ciro matan daga cikin ramin, sai dai likitoci sun tabbatar da mutuwarsu. Daga nan aka mika gawarwakin ga jami’in ‘yan sanda na Caji Ofis ɗin Gezawa, Musa Garba, domin ci gaba da bincike da kuma daukar matakan doka.

Sanarwar ta ƙara da bayyana cewa matan sun faɗa cikin kudiddifin ne a yayin da suka je su ɗauraye jikinsu, bayan sun kammala aiki a wani kamfanin sarrafa zoɓo da ke yankin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending