News
Rigimar Fili: Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Zargin Malamai Da Badaƙalar Fili Mai Darajar N3.5bn A Kano
Wata babbar kotu a jihar Kano ta sanya ranar 23 ga watan Mayu domin yanke hukunci kan wata ƙara da ƙungiyar Musabaqah Association ta shigar gabanta, inda take neman dakatar da hukumar EFCC daga cigaba da binciken wasu malamai kan zargin hada baki wajen siyar da fili mai darajar Naira biliyan 3.5.
Ƙungiyar ta shigar da ƙarar ne biyo bayan gayyatar da EFCC ta yi wa wasu daga cikin membobinta don amsa tambayoyi game da yadda aka yi amfani da wani fili da gwamnatin Kano ta ba su tun shekarar 1995 domin gina makarantar horas da ɗaliban Musabaƙar Al-Qur’ani mai girma.
Rahar Da Buhari Ya Yi Wa Atiku A Kaduna Ta Haifar Da Cece-kuce
A cewar masu shigar da ƙarar, filin wanda ke a unguwar Nassarawa GRA, kusa da Ahmadu Bello Way, yana da girman hekta biyu, kuma an ba su ne a matsayin tallafi domin amfanin Musabaƙar Al-Qur’ani, ciki har da gina masallaci, wurin kwana, ɗakunan karatu da shaguna.
Sai dai bisa ga binciken da aka gudanar, an gano cewa gidaje kusan 38 ne aka gina a kan filin da nufin sayar da su, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin mambobin ƙungiyar. Masu ƙarar sun ce an siyar da filin ga kamfanin Nata’ala Properties and Investment Company Limited a kan farashin Naira miliyan 400 kacal, duk da cewa darajar filin ta kai Naira biliyan 3.5.
“Wannan wata badakala ce da ke nuna alamun damfara. Ba za mu lamunta da hakan ba. Muna so a binciko gaskiyar lamarin tare da hukunta masu hannu a ciki,” in ji masu ƙarar.
Sun bayyana cewa malaman da ake zargi da hannu wajen siyar da filin sun haɗa da Ibrahim Shehu-Maihula, Gwani Yahuza-Danzarga, Aliyu Harazim, Tijjani Bala-Kalarawi, Sa’idu Muhammad-Koki da Ado Shehu-Maibargo. Sauran sun haɗa da Abdu Muhammad-Dutse, Abubakar Aliyu-Darma, Ahmad Tijjani-Yusuf, Tijjani Mailafiya-Sanka, Sabiu Bako da Muhammad Tukur-Gadanya.
Tun bayan bankaɗo batun a cikin wani shirin rediyo mai suna Rigar Kaya a watan Agusta na 2023, wanda Yakubu Musa Fagge ke gabatarwa, lamarin ya dauki hankalin jama’a, inda aka zargi wasu daga cikin shugabannin ƙungiyar da yin raba filin cikin tsarin haɗaka da kamfanin Nata’ala – inda aka ware gida 8 ga kwamitin Musabaqah, yayinda sauran 30 suka kasance na kamfanin.
Daga bisani, wasu daga cikin mambobin ƙungiyar sun ƙi amincewa da wannan tsari, lamarin da ya kai su ga shigar da ƙara a gaban EFCC da kuma kotu domin kare haƙƙinsu da hana gayyatar EFCC.
Mai shari’a Musa Shuaibu ya bayar da damar sasanci tsakanin bangarorin, amma ya tsayar da ranar 23 ga Mayu domin yanke hukunci kan ko hukumar EFCC na da hurumin cigaba da gayyatar malamai da ake zargi.
