News
An Kama Fiye Da Mutum 500 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka Daban-Daban A Kano

A wani samame na hadin gwiwa da hukumomin tsaro suka gudanar a fadin Jihar Kano, an cafke fiye da mutum 500 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da dabanci, fashi da makami, da fataucin miyagun kwayoyi. Haka kuma, an samu nasarar kwace miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai Naira miliyan 300.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, ya bayyana cewa sama da mutum 150 daga cikin wadanda aka kama, suna da hannu cikin manyan laifuka da suka hada da kwacen waya da barna a cikin gari. Ya ce wannan aikin na musamman ya gudana ne a kananan hukumomi takwas na birnin Kano, bisa bayanan sirri da aka samu daga jami’an tsaro da al’umma.
TA’ADDANCI A ZAMFARA: ‘Yan Bindiga Sun Kona Masallacin Juma’a, Asibiti Da Gidaje
Aikin, wanda aka yi tare da hadin gwiwar hukumar NDLEA, NSCDC, hukumar kula da gidajen yari, hukumar shige da fice, da sauran hukumomi, ya zama wani muhimmin mataki na yaki da ta’addanci da kuma matsalolin da ke addabar matasa.
Shugaban Kwamitin Dawo da Zaman Lafiya da Kyautata Dabi’un Matasa, Dakta Yusuf Ibrahim, ya bayyana cewa kwace miyagun kwayoyin zai rage yawaitar laifuka da kuma kawo sauki ga rayuwar al’umma, musamman matasa. Ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin al’umma da hukumomin tsaro domin dorewar zaman lafiya.
Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam, ya yaba da nasarorin da aka samu, tare da bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace domin dakile kalubalen tsaro.
Kwamishinan ‘yan sanda ya bukaci kafa kotun musamman domin hanzarta shari’ar wadanda ake zargi, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage cunkoso a gidajen yari da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar. Haka zalika, kwamandan NDLEA, Abubakar Idris, ya nemi ci gaba da hadin gwiwar da ke tsakanin hukumomin tsaro don dorewar nasarorinda aka samu.