News
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum Biyu, Sun Yi Garkuwa Da Mutum 50 A Ƙauran Namoda
A jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, mazauna garuruwan Banga da Gidan Giji da wasu yankuna a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda na fuskantar halin ƙaura sakamakon tsananin hare-haren da ƴan bindiga ke ci gaba da kai musu.
A farkon makon nan, wasu ƴan fashin daji sun afka wa garuruwan inda suka kashe aƙalla mutum biyu tare da yin garkuwa da kusan mutum hamsin — ciki har da maza da mata. Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun nemi a biya su naira miliyan ɗari a matsayin kuɗin fansar waɗanda suka sace.
An Kama Fiye Da Mutum 500 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka Daban-Daban A Kano
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa: “Sun zo da babura dauke da makamai, sun mamaye garinmu, sun kama yara da manya, sun kashe mutum biyu, sannan suka tafi da mutum 50. Da ba don jaruntakar jami’an Vigilantee ba, da lamarin zai fi haka muni.”
Har yanzu ba a samu wata sanarwa daga gwamnatin jihar Zamfara ba kan wannan hari, duk da ƙoƙarin da kamfanin BBC ya yi don jin ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar, Suleiman Bala.
Rahoton kamfanin Beacon Security Intelligence ya nuna cewa a watan Maris 2025 kadai, mutum 179 ne aka kashe a Zamfara, wanda ya sanya ta zama jiha ta biyu mafi yawan asarar rayuka sakamakon ta’addanci a Najeriya — ƙasa da Katsina da ta samu mutum 302 da aka kashe a watan Fabarairu.
Zamfara na ci gaba da zama daya daga cikin jihohin da ke fama da matsanancin rashin tsaro, duk da ikirarin hukumomin tsaro na samun nasarori a kan ƴan bindigar da suke adabar yankunan.
