News
TA’ADDANCI A ZAMFARA: ‘Yan Bindiga Sun Kona Masallacin Juma’a, Asibiti Da Gidaje
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari garin Biyabiki da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, inda suka kona masallacisn Juma’a, asibitin kula da lafiyar farko da kuma gidaje sama da goma a ranar Asabar da misalin karfe 8 na dare.
Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa harin na iya zama ramuwar gayya daga mabiyan wani sanannen shugaban ‘yan bindiga, Adamu Aliero, bayan hallaka dan uwansa Isuhu Yellow da dansa a wani artabu da jami’an tsaro makonni uku da suka wuce a yankin Keta.
Wani mazaunin garin da ya nemi a boye sunansa saboda tsaro ya shaida cewa: “Ba su kashe ko kama kowa ba, amma sun kona wurare da dama ciki har da masallacin Juma’a da asibitin unguwa. Hakanan sun rusa gidaje akalla goma.”
Mazauna yankin sun bayyana fargabarsu kan yadda hare-haren ke kara ta’azzara tun bayan rasuwar Isuhu Yellow. “Tun bayan mutuwarsa muke fama da hare-hare iri-iri. Muna zargin wannan wani bangare ne na daukar fansa,” in ji wani mazaunin yankin.
Kokarin da aka yi don jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ci tura, domin bai dauki kiran wayar da aka masa ba.
Wannan hari na baya-bayan nan yana ci gaba da jaddada yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a jihar Zamfara, duk da ayyukan rundunar soji da sauran jami’an tsaro a yankin.
