Connect with us

Opinion

El-Rufa’i Ba Zai Iya Kwatanta Gwanin Siyasa da Kwankwaso Ba” — Bashir A. Bashir

Published

on

IMG 20250415 WA0020
Spread the love

Comrade Bashir A. Bashir, hadimin kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ba zai taɓa iya kwatanta irin hazaka da gwanintar siyasa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke da ita ba.

‎Bashir ya ce, “Kwankwaso ba kawai jama’a ke biye masa bane, akwai wata baiwa ta musamman da Allah ya hore masa da take sanya shi zama zakaran gwajin dafi a fagen siyasar Najeriya.”

Kotu Ta Yanke Wa Matashi Hukuncin Shekara Daya A Gidan Yari Kan Satar Keke 

‎Ya ci gaba da cewa, duk da irin shaharar El-Rufa’i a arewacin Najeriya, ba zai iya shiga sahun Kwankwaso ba wajen karɓuwa a zukatan jama’a da kuma kwarewa a tafiyar da harkokin siyasa.

Advertisement

‎Wannan jawabi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara a kafafen sada zumunta kan irin tasirin da manyan ‘yan siyasar arewa ke da shi, musamman a shirye-shiryen zabukan gaba.

‎Comrade Bashir ya kammala da cewa, “Kwankwasiyya ba ƙungiya bace kawai — falsafa ce, ra’ayi ne, da kuma motsi na kwarai da ke da tushen karɓuwa daga al’umma. Wannan wani abu ne da babu wanda zai iya kwaikwaya.”

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *