News
Za a Kashe Ɓeraye A Garun Malam Domin Hana Yaduwar Cutar Lassa – Gwamnatin Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta fara wani gagarumin mataki na kashe Ɓeraye a karamar hukumar Garun Malam, a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar Lassa da aka tabbatar da bullarta a yankin.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis. Ya ce matakin ya zama dole ne domin kare lafiyar al’umma bayan da aka samu tabbacin rasuwar wata mata sakamakon kamuwa da cutar Lassa a Garun Malam.
Tsohon Alkalin Babban Kotun Kano, Mai Shari’a Wada Umar Rano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 75
“Bincike ya tabbatar da cewa mijin marigayiyar da ɗaya daga cikin ’ya’yanta suma sun kamu da cutar. Tuni aka killace su tare da sauran mutanen da suka yi mu’amala da ita,” in ji Kwamishinan.
Dr. Labaran ya bayyana cewa Ɓeraye na daga cikin manyan hanyoyin da cutar Lassa ke yaduwa, don haka kashe su a yankin da aka samu bullar cutar wata hanya ce ta dakile ci gaban yaduwar.
Ya kuma ja hankalin mafarauta da su guji farautar Ɓeraye, tare da daukar matakan kariya domin hana yada cutar daga dabbobin zuwa ga mutane.
Kwamishinan ya bukaci al’umma da su rika kai rahoton duk wani zargin cutar Lassa ga cibiyoyin lafiya mafi kusa, tare da kira ga jami’an lafiya da su ci gaba da bin matakan kariya yayin da suke kula da masu fama da cutar.
Sanarwar ta kuma bukaci hadin kan jama’a wajen tabbatar da nasarar wannan mataki na gaggawa da gwamnati ke dauka domin kare lafiyar al’ummar jihar.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
