Sports
Xabi Alonso Na Dab Da Ajiye Aiki A Ƙungiyar Bayer Leverkusen, Domin Komawa Horar Da Real Madrid

Rahotanni daga Jamus na cewa kocin Bayer Leverkusen, Xabi Alonso na dab da ajiye aiki a ƙungiyar, domin komawa Real Madrid ta Sifaniya don maye gurbin Carlo Ancelotti.
A ƙarshen kakar bana ne Alonso zai yi ƙaura, kasancewar yana da damar amfani da wata saɗara a kwantiraginsa da leverkusen inda zai koma Madrid a matsayin koci mara ƙungiya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Taya Dangambo Murnar Zama Shugaban Online Media Chapel
Ita kuwa Real Madrid tana fuskantar kakar wasa ba tare da ɗaga kofi ba a bana, bayan an fitar da ita daga gasannin Zakarun Turai da na Copa Del Rey.
A yanzu La Liga ce ta rage mata, amma sai idan ta iya cim ma Barcelona, wanda abu ne mai matuƙar wahala ganin cewa wasanni biyar ne suka rage kafin kammala gasar.
Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti yana shan suka kan raunin da ƙungiyar ta samu, kuma ana kyautata zaton zai bar ƙungiyar, inda kocin Leverkusen ke kan gaba a jerin masu neman kujerarsa.
Ancelotti zai koma horar da tawagar ƙwallo ta ƙasar Brazil, bayan da rahotanni suka bayyana cewa ya samu tayi daga hukumomin ƙwallo na ƙasar.