Connect with us

News

Muhimmancin sada zumunci – Malam Jafar

Published

on

DAGA Sheikh Ja’afar Haruna Ja’afar Dutsen-wai

Sada zumunci shi ne kyautatawa da jinƙai da bibiyar ’yan uwa (ma’abota zumunci), ta hanyar sadar da dukan alheri garesu, da kawar da dukan sharri daga gare su gwargwadon iko.

Advertisement

Ziyartarsu da amsa kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu’ar alheri, duk ɓangare ne na sada zumunci.

Majalisar Wakila na nazari kan ƙudurin kafa ƙarin jami’o’i 47 a Najeriya 

Har ila yau, ma’anar zumunci na game yin sallama ga ɗan uwa yayin haɗuwa da gaishe shi da ce masa Yarhamukallahu idan ya yi atishawa ya ce alhamdulillahi.

Advertisement

Sannan zuwa duba dan uwa yayin da yake rashin lafiya da jajanta masa kan wata asara da ya yi da taya shi farin cikin samun wani alheri da rufa masa asiri da riqe amanarsa da kare mutunci da martabarsa a kan idonsa ko a bayansa a ɓoye ko a bayyane da yi masa nasiha da shawara ta alheri duk sada zumunci ne.

Hukuncin sada zumunci:

Advertisement

Wajibi ne Musulmai su sada zumuncin da ke tsakaninsu, kamar yadda shiryarwar Musuluci ta ginu kan haka, Allah Ta’ala Yana cewa, “ka tuna lokacin da muka riki alkawari daga Banu Isra’ila cewa kada su bauta wa kowa sai Allah, kuma su kyautata ga iyaye da ma’abucin zumunci (’yan uwa) da marayu da miskinai, kuma ku gaya wa mutane kyakkyawan zance, kuma ku tsai da Sallah ku bada Zakka, sai kuka juya baya (ga barin wannan umarni), sai ’yan kaɗan ne daga cikinku, kuna masu bijirewa.”

Kuma a suratul Bakara, aya ta 27 Allah Ya fassara fasiƙai a cikin faɗinsa, “su ne masu warware alƙawarin Ubangiji (kan aiko Annabi SAW), bayan ƙarfafa alqawarin gare su, kuma suke yanke abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi (zumunci), kuma suke ɓarna a bayan ƙasa, waɗannan su ne taɓaɓɓu.”

Advertisement

 

Ma’abuta zumuci:

Advertisement

 

Su ne duk makusantan mutum (na jini) na kusa ko na nesa, magadansa ne ko ba magada ba, muharramai ne ko ba muharramai ba, masu dangantaka da shi da suka haɗa da kakanni da iyaye da ’ya’ya da jikoki, ’yan uwa maza ko mata kanne da yayye da ’ya’yansu da ’yan uwan uba da na uwa.

Advertisement

 

 

Advertisement

Idan muka faɗaɗa ma’anar zumunci zuwa ga ’yan uwantakar Musulunci da bada haƙƙi ga ma’abutansa, to kai-tsaye, aya ta 36 a Suratun-Nisa’i, za ta yi mana jagoranci ga raba ma’abuta haƙƙin kyautatawa zuwa gida uku, inda Allah Maɗaukaki Yake cewa, “kuma ku bauta wa Allah, kada ku haɗa wani da shi a cikin bauta (shirka), kuma ku kyautata ga iyaye da ma’abucin zumunci da marayu da miskinai da maƙwabci ma’abucin zumuncin da makwabci manisanci da aboki a gefe da ɗan tafarki da bayinku. Haƙiƙa Ubangiji ba Ya son wanda ya kasance mai taƙama, mai yawan alfahari.”

Bisa koyarwar wannan aya, za mu iya raba ma’abuta haqqin a kyautata musu zuwa gida uku:

Advertisement

a) Mutum mai haqqi uku: ɗan uwa na jini Musulmi kuma makwabci.

 

Advertisement

b) Mautum mai haƙƙi biyu: Musulmi kuma makwabci

 

Advertisement

c) Mutum mai haƙƙi zaya: makwabci a gida ko a kasuwa ko abokin tafiya da ba Musulmi ba.

Falalar sada zumunci:

Advertisement

 

Falalar sada zumunci ba za ta kayyaɗu ba, sai dai kawai a faɗi kaɗan daga ciki:

Advertisement

Tsawaitar rayuwa.

 

Advertisement

Wadatar zuciya.

 

Advertisement

Bunƙasar dangi.

 

Advertisement

Tsallake Siraɗi cikin sauƙi.

 

Advertisement

Samun yardar Allah.

 

Advertisement

Samun haɗin kai.

 

Advertisement

Samun shiga Aljanna da sauransu.

 

Advertisement

Uƙubar yanke zumunta:

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, shi ne abin da za mu iya cewa, saboda abin da ya samu zumunci na ɓalɓalcewa, babu zumunci, ɗan uwa ya ga ɗan uwansa, kowa ya shige, saboda rashin sani, ko a kan sani. Ba a zumunci, mai kuɗi don girman kai da ganin sai dai shi a zo masa, talaka kuma don tsoron wulaƙanci, talaka da talaka kuma don tsoron kada ya ɗora wa ɗan uwansa nauyi.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Ayoyi da Hadisai da dama, sun ja kunne kan yanke zumunci. Ma’aiki (SAWW) ya ce, “mai yanke zumunci ba zai shiga Aljanna ba.”

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hanyoyin sada zumunci:

 

Advertisement

Ana sada zumunci ne ta hanyoyi da dama, kamar tattaki zuwa wurin ’yan uwa ko wasiqa ko wayar sadarwa ko saƙon baka (a aika gare) ko shirya tarurrukan taya farin ciki ko jajanta wa wani.

 

Advertisement

Allah Ya inganta zumuncin da ke tsakanin Musulmi, ya kuma ba mu damar cigaba da sada zumunci da ’yan uwanmu, Ameen.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending