Connect with us

News

Shugaba Tinubu Baya So A Yi Zaɓe So Yake A Nada Shi Shugaban Kasa Kamar Yadda Ake Nada Sarki —Dino Melaye

Published

on

dino and tinubu 768x432

Tsohon Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya zargi Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da yunƙurin tauye dimokuraɗiyya a ƙasar, yana mai cewa ana ƙoƙarin karkatar da tsarin zaɓe zuwa irin na sarauta.

Melaye ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television a shirin The Morning Brief, inda ya ce gwamnatin jam’iyyar APC na ƙoƙarin haddasa rikice-rikice a cikin jam’iyyun adawa, ciki har da ADC.

Advertisement

Rundunar Sojin Najeriya Ta Musanta Zargin Cewa Sojoji Sun Taimaka Wa ‘Yan Ta’addan Da Suka Kai Hari A Filato

A cewarsa, waɗannan matakai na nuni da wani shiri na raunana adawa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Advertisement

“Abin da ke faruwa ba wai batun jam’iyya guda ba ne, illa barazana ce ga dimokuraɗiyyar Najeriya baki ɗaya,” in ji Melaye.

Ya ƙara da cewa shugaban ƙasar na da burin a sake dawowa da tsarin mulki irin na gargajiya, inda ba za a gudanar da zaɓe na gaskiya ba.

Advertisement

“Shugaba Tinubu ba ya son zaɓe, yana son a naɗa shi kamar sarki,” a cewar Melaye.

Sai dai kawo yanzu, babu wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ko jam’iyyar APC dangane da waɗannan zarge-zarge.

Advertisement

Masu lura da harkokin siyasa na ci gaba da bayyana damuwa kan irin waɗannan kalamai, yayin da ake tunkarar zaɓukan gaba a ƙasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending