Connect with us

News

Rundunar Sojin Najeriya Ta Musanta Zargin Cewa Sojoji Sun Taimaka Wa ‘Yan Ta’addan Da Suka Kai Hari A Filato

Published

on

file 00000000fddc720ab21e370dffec9735 750x375

Dakarun rundunar haɗin guiwa ta ofureshan Enduring Peace, ta yi watsi da zargin da ake mata na taimaka wa mahara a lokacin da suka kai mummunan hari Angwan Rukuba a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.

Rundunar sojin ta bayyana zargin – wanda ake alaƙantawa da shugaban matasan garin wanda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta – da marar tushe.

Advertisement

Gwamnatin  Kano Ta Tura Dalibai 550  Domin Taimakawa Wajen Faɗaɗa Rajistar Katin Zaɓe A Fadin Jihar ‎

“Babu wani lokaci da dakarun sojin ta kowacce fuska domin bai wa ‘yan ta’adda kariya a lokacin kai mummunan hari,” a cewar jami’in yaɗa labaran rundunar, Chinonso Oteh, a cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Talata.

Advertisement

Martanin na zuwa ne bayan labarai masu cin karo da juna da ake yaɗawa bayan harin na ranar Lahadi.

Mista Oteh ya ce, dakarun sun mayar da martani nan take bayan samun kira kan lamarin, sai dai kafin su isa wurin, ‘yan ta’addan sun gudu.

Advertisement

“dakarunmu sun samu kira…kuma nan da nan aka tura su wurin da abin ke faruwa wanda ke nesa daga inda muke, sai dai maharan sun gudu kafin mu ƙarasa,” ya faɗa.

Ya kuma ce sojojin sun yi ƙoƙarin daƙile ayyukan maharan amma ba su yi nasara saboda guduwa da maharan suka yi.

Advertisement

“Dakarunmu sun yi aiki cikin ƙwarewa domin daƙile harin wanda da zai dakatar da zubar da jini da ‘yan ta’addan da suka gudu suka yi,” ya bayyana, yana mai cewa waɗanda suka tsallake rijiya da baya da sauran jami’an tsaro shidu ne kan wannan ƙoƙari da jami’an suka yi.

A cewar rundunar sojin, an tura manyan motocin dokon bindigu zuwa yankin kuma tuni ta bincika zargin da ake yi wa dakarunta amma ta tarar ba gaskiya ba ne.

Advertisement

Jawabin na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da yamutsa hazo biyo bayan harin Jos wanda ya jawo aka sa awa dokar hana zirga-zirga na awa 48 da gwamnatin Filato ta saka da sake. Wannan mataki ya jawo sake jadalin rubuta jarrabawa da za a yi a jami’ar Jos saboda matsalar tsaro.

Sannan al’umma sun yi suka game da jinkiri da aka samu wajen kawo ɗauki da ɗaukacin yawan afkuwar tashe-tashen hankula a jihar Filato.

Advertisement

Runduna ta ce irin wannan ƙirari da akke yi zai iya dakushe ƙoƙarin da rundunar ke yi. Mista Oteh ya bayyana zargin shugaban matasa da abu da ka iya “dakushe hazakar dakarun sojar tare rashin son juna tsakaninsu sojoji da al’umma.”

Ya kuma buƙaci mazauna garin da su mayar da hankali wajen tallafa wa jami’an tsaro da sahihan bayanai, yana mai cewa suna ƙoƙarin ganin sun kama waɗanda suke da hannu wajen kai hari.

Advertisement

“Dakarunmu suna amfani da dabaru masu tasiri domin kama waɗanda suka kai mummunan harin,” ya faɗa.

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending