News
Iran Ta Yi Ruwan Makamai Masu Linzami Kan Isra’ila

An wayi gari a ranar Litinin da cigaba da luguden wuta tsakanin kasashen Iran da Isra’ila, wanda ya barke tun ranar Juma’a bayan da Isra’ila ta kai hari kan Tehran.
Iran ta mayar da martani ta hanyar ruwan makamai masu linzami kan biranen Isra’ila da suka hada da birnin Haifa, inda cibiyar makamashi take.
Shugaba Tinubu Ya Ba Da Umarnin Gaggauta Dakile Rikicin Jihar Benue
A nata bangaren, Isra’ila ta tashi da jiragen yakin ta inda ta kai hare-hare a kan wasu wurare a kasar Iran ciki har da ma’aikatar harkokin wajen kasar.
Rahotanni daga Isra’ila sun nuna cewa mutum hudu ne suka rasa rayukansu, tare da rushewar wasu gine-gine a birane daban-daban.
Iran ta bayyana cewa dakarun juyin juya halinta ne suka kaddamar da farmakin safiyar Litinin, inda ta ce an kai hare-haren ne a wurare na musamman.
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa kasar sa ba ta da niyyar kera makaman nukiliya, kuma tana da ‘yancin ci gaba da amfani da makamashi na nukiliya don ci gaban tattalin arziki. Ya kara da cewa jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei, bai amince da sarrafa makaman kare dangi ba.
Rahotanni da suka zuwa yanzu sun bayyana cewa Iran ta rasa mutane 224 yayin da Isra’ila ta yi asarar mutane 18.
Wannan sabon rikici na kara jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin hali na fargaba da kuma kira daga kasashen duniya da su shiga tsakani don dakile barkewar yaki gaba daya.