Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Ba Da Umarnin Gaggauta Dakile Rikicin Jihar Benue

Published

on

Tinubu
Spread the love

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarni na musamman ga hukumomin tsaro na ƙasa da su gaggauta ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen rikicin da ke ci gaba da ƙama da rayuka a jihar Benue, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 200.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Lahadi, yana mai cewa shugaban ƙasan ya umurci jami’an leƙen asiri, rundunar ‘yan sanda da na sojoji da su hanzarta isa jihar domin gudanar da atisayen dawo da doka da oda.

Majalisa Na Shirin Ƙara Yawan Alƙalan Kotun Ƙoli Zuwa 30

“Shugaban ƙasa ya nuna damuwa matuƙa game da rikicin, kuma ya ce dole ne hukumomin tsaro su tashi tsaye domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar,” in ji Onanuga.

Advertisement

Shugaban ƙasa Tinubu ya kuma umarci gwamnan jihar Benue, Reverend Father Hyacinth Alia, da ya jagoranci shirya zaman sasanci tsakanin ɓangarorin da ke rikici, musamman tsakanin manoma da makiyaya da sauran al’ummar yankin.

A cewar sanarwar, Tinubu ya bayyana kashe-kashen da ake yi a jihar a matsayin abin takaici da rashin imani, yana mai cewa irin waɗannan ayyuka na jefa ƙasa cikin koma baya.

“Ya kamata shugabannin siyasa da na al’umma su guji furta kalaman da za su iya tunzura jama’a ko haddasa tarzoma. Ya zama wajibi a cafke kuma a hukunta duk wanda aka samu da laifin tayar da zaune tsaye ko ramuwar gayya,” in ji Shugaban Ƙasa.

Advertisement

A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, rahotanni sun nuna cewa daruruwan mutane sun rasa rayukansu a wasu sassan jihar Benue, sakamakon tashe-tashen hankula da suka haɗa da hare-haren kwanton bauna da kisan gilla, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin al’umma da ƙara matsa lamba kan gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakin kawo ƙarshen rikicin.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *